1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mali ta yi sabon firaminista

Yusuf BalaJanuary 9, 2015

Cikin mulkinsa na watanni goa sha bakwai shugaba Boubacar Keita ya sauya firaminista har sau uku a wannan kasa ta Mali da lamarin tsaronta ke cikin rudani.

https://p.dw.com/p/1EI0P
Ibrahim Boubacar Keita auf dem USA-Afrika-Gipfel
Hoto: picture alliance/AP Photo

Shugaban kasarta Mali ya maye gurbin fiiraministan kasar da wani mai shiga tsakani daga bangaren gwamnati yayin tattaunawa da 'yan tawaye a arewacin kasar. A yammacin jiya Alhamis ne dai gwamnatin kasar ta bayyana Modibo Keita dan shekaru 73 a matsayin wanda zai maye gurbin firaminista Moussa Mara mai barin gado.

Wannan dai shi ne karo na uku da shugaba Ibrahim Boubacar Keita ke zabin firamnista tun bayan da ya hau karagar ulki watanni 17. Kasar dai ta Mali ta shiga hali na rudani tun bayan juyin mulki a watan Maris na shekarar 2012 abin da ya bada dama ga 'yan Al kaida da wasu masu jihadi suka karbi iko da arewacin kasar.