Mali ta yi maraba da tura dakaru kasar | Labarai | DW | 13.11.2012
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mali ta yi maraba da tura dakaru kasar

Jami'an gwamnatin kasar Mali sun yi maraba da shirin kasashen yammacin Afirka na tura dakaru domin kwato arewacin kasar daga 'yan tawaye.

Jami'an gwamnatin ƙasar Mali sun yi maraba da shirin shugabannin ƙasashen yankin Yammacin Afrika na ECOWAS, na tura dakaru 3,300 domin sake kwato yankin arewacin ƙasar daga hanun 'yan tawaye.

Ministan tsaron ƙasar Kanar Yamoussa Camara, ya ce yanzu ta tabbata ƙarara lokaci ya ƙure wa 'yan tawayen. Yanzu haka shirin na jirar amincewar ƙudirin Majalisar Ɗinkin Duniya, kuma ministan ya ce nan zuwa watan gobe na Disamba, ya na saran ayi amfani da ƙarfin wajen kawar da 'yan tawayen.

Amma a ɗaya hanun ƙasar Algeriya, mai makwabtaka da yankin na arewacin Mali, ta sabunta kirar ganin anyi amfani da hanyoyin tattaunawa maimakon nuna ƙarfin soja. Taron shugabannin ƙasashen yankin na Yammacin Afirka da aka gudanar ƙarshen mako a birnin Abuja na Tarayyar Najeriya, ya amince da shirin tura dakarun, bisa amincewar Majalisar Ɗinkin Duniya, wadda ake jira ta bayar da dama ta ƙarshe.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Umaru Aliyu

 • Kwanan wata 13.11.2012
 • Muhimman kalmomi Mali
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/16hcd
 • Kwanan wata 13.11.2012
 • Muhimman kalmomi Mali
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/16hcd