Mali ta cimma yarjejeniya tsakanita da 'yan tawaye
February 20, 2015Talla
An dai cimma wannan yarjejeniya a jiya Alhamis a ƙarƙashin jagorancin Majalisar Ɗinkin Duniya a birnin Algers na Aljeriya.
Ƙungiyoyin da suka saka hannu a kan yarjejeniyar su ne Ƙungiyar 'yan tawaye ta abizinawa ta AZAWAD wato MNLA da Ƙungiyar CM-FPR da kuma wasu ƙungiyoyin guda biyar.Ministan harkokin waje na Aljeriya Ramtane Lamara ya ce dukkanin ɓangrorin sun amince su dakatar da fadan.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman