1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mali ta aike da sojoji garin Kidal

Ahmed Salisu
February 10, 2020

Dakarun Mali a wannan Litinin din sun fara kama hanyarsu ta zuwa garin Kidal a arewacin kasar domin tinkarar 'yan tawayen da masu da'awar jihadi da suka dau tsawon lokaci suna cin karensu babbaka a wajen.

https://p.dw.com/p/3XZVb
Mali Unruhen l Erneuter Angriff auf Soldaten - Symbolbild
Hoto: Imago/Le Pictorium/N. Remene

Shugaban Mali din Ibrahim Boubacar Keita ne ya ambata hakan a wata hira da wata kafar watsa labarai ta kasar Faransa ta yi da shi, inda ya ce wannan mataki da suka dauka abu ne mai kyau.

Wannan batu na tura sojin na Mali garin na Kidal dai na daga cikin irin abubuwan da aka cimma a yarjejeniyar nan ta wanzar da zaman lafiya da aka yi a birnin Algiers tsakanin gwamnatin kasar da 'yan tawaye a shakarar 2015.

Dubban sojoji da fararen hula ne dai suka rasa rayukansu a tun bayan da Kidal din ta fadi daga hannun gwamnati a shekarar 2012 wanda hakan ya haifar da kalubalen tsaro a kasashen da ke makotaka wanda suka hada da Burkina Faso da Nijar.