Mali: Sojoji sun kashe ′yan ta′adda | Labarai | DW | 04.03.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mali: Sojoji sun kashe 'yan ta'adda

Rundunar sojan Mali ta dakile wani mumunan harin mayakan jihadi a garin Dinangourou da ke kan iyakar kasar da Burkina Faso tare da kashe maharan takwas.

Rundunar ta ce ta yi nasarar tarwatsa wasu muggan makamai daga maharan baya ga kwace motarsu, da kuma wasu babura guda hudu daga mayakan, sai dai sanarwar ta ce an kashe wani sojan kasar daya a yayin da uku suka ji mumunan rauni.

Ko a ranar 23 ga watan da yagaba wani harin kwantar bauna ya hllaka sojojin Mali biyu tare da raunata wasu bakwai a kauyen Sévaré da Konna da ke tsakiyar kasar.