1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnatin Mali ta bayyana shirin matakan tsaro a Ogossagou

Abdoulaye Mamane Amadou
March 25, 2019

Kwanaki bayan kisan fararen hula 130 hukumomin kasar Mali sun bayyana daukar matakai na tsaro a wani yunkuri na kare jama'a

https://p.dw.com/p/3FeKP
Frankreich Paris 2018 | Ibrahim Boubacar Keita, Präsident Mali
Hoto: picture-alliance/dpa/Maxppp/Mousse

Shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita ya kai ziyarar gani da ido a yau Litinin a kauyen Ogossagou da ke yankin tsakiyar kasar inda aka yi wa  fulani fararen hula kisan kiyashi a karshen makon jiya. Akalla Fulani 130 ne suka mutu galibi mata da yara sakamakon wani harin da mayakan sa kai 'yan kabilar Dogons suka kai a garin na kabilar Fulani zalla.