SiyasaJamus
Rikici ya barke a tsakanin kungiyoyin ta'adda
September 7, 2022Talla
Rahotanni daga kasar Mali sun tabbatar da labarin rikicin da ya barke a tsakanin kungiyoyin 'yan ta'adda da ke gaba da juna, inda daga bisani Kungiyar IS ta yi nasarar kwace ikon garin Talataye da ke karkashin ikon 'yan tawayen Azawad na 'yan kabilar Touareg da suka yi kaka-gida a yankin arewacin kasar.
Wani jami'in tsaro na yankin da bai yarda a fadi sunansa ba, ya ce, an kwashi fiye da sa'oi uku ana gwabza fadan, amma kawo yanzu mahukuntan Malin ba su yi tsokaci kan fadan dama irin asarar da aka tafka ba. Kasar Mali ta shafe shekara da shekaru tana fama da munanan hare-haren mayakan jihadi da suka addabi kasashen yankin Sahel, musamman jamhuriyar Nijar da Burkina-Faso da ke makwabtaka da Malin.