1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mali: An halaka Fulani a fadan kabilanci

Gazali Abdou Tasawa MNA
January 2, 2019

A kasar Mali mutane 37 ne suka halaka a kauyen Fulani na Koulogon na tsakiyar kasar a sakamakon wani hari da wasu maharban gargajiya suka kai masu a ranar Talata.

https://p.dw.com/p/3AsbR
Mbororo Nomaden aus dem Wodaabe Stamm
Hoto: cc-by-sa/Dan Lundberg

A cikin wata sanarwa da gwamnatin kasar Mali ta fitar a yamamcin ranar Talata ta ce maharan wadanda aka fi sani da maharban Dozos na kabilar Dogon sun kuma jikkata fararan hula da dama tare da kone gidaje masu yawa. 

Gwamnatin kasar ta Mali dai ta sanar da cewa za ta dauki matakin gurfanar da wadannan mahara a gaban kuliya domin fuskantar hukuncin doka, kana ta ce za ta karfafa matakan tsaro a yankin. 

Wannan hari ya zo ne a daidai lokacin da gwamnatin kasar ta Mali ta kaddamar da wani shiri na neman sasanta kabilun yankin da suka jima suna zaman doya da man ja a tsakaninsu.

Mutane sama da 500 ne suka halaka a cikin fadan kabilanci a kasar ta Mali a shekara ta 2018 da ta shude.