1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin kabilanci ya lakume rayuka 95

Ramatu Garba Baba
June 11, 2019

Ana cikin zaman zulumi biyo bayan asarar rayuka da aka tafka a sanadiyar rikicin kabilanci da ya barke a kauyen Dogon inda mutane fiye da 95 suka halaka.

https://p.dw.com/p/3K9lI
Mali | Kuhherde in Segou
Hoto: Imago Images/Le Pictorium/N. Remene

An zargi maharan da cinna wa kauyen wuta bayan da suka kashe mutanen a yayin harin. Majalisar Dinkin Duniya ta yi alla-wadai da harin da ya jefa kasar cikin yanayi na jimami, inda ta bukaci bangarorin da lamarin ya shafa da su guji kai hari irin na ramuwar gayya. Gwamnatin kasar ta sha lawashin gudanar da bincike don gano wadanda ke da hannu a wannan aika-aikan.

Ko a watan Maris na wannan shekarar, mutum dari da hamsin ne suka mutu bayan wani fada a tsakanin mafarauta da Fulani a kauyen na Dogon, harin da aka ce shi ne mafi muni a tarihin kasar ta Mali.