Mali na bukatar sojojin mayar da martani | Labarai | DW | 08.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mali na bukatar sojojin mayar da martani

Bayan dakarun Nijar da suka rasu a Mali har yanzu ana samun mace-macen dakarun wanzar da zaman lafiya a yankin arewacin Mali

Kasar Mali ta bukaci Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya da ta aika mata da sojojin mayar da martanin gaggawa su taimaka mata wajen kwantar da hare-haren da ake kaiwa dakarun wanzar da zaman lafiyar Majalisar Dinkin Duniyar ba kakkautawa a yankin arewacin Mali, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 31.

Ministan harkokin wajen Mali Abdoulaye Diop ya fadawa Kwamitin mai mambobi 15 cewa tilas ta dauki matakan gaggawa, wadanda za su tabbatar da cewa Majalisar ta gudanar da ayyukan da za su kare muradunta na kula da rayukan fararen hula, musamman ganin yadda dakarun wanzar da zaman lafiyan ke jin shi a jika wajen gudanar da ayyukansu