1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An hallaka mutun 580 a Mali

Abdoulaye Mamane Amadou
June 26, 2020

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa an hallaka mutane fiye da 500 a yankin tsakiyar Mali sakamakon fadace-fadacen kabilanci ko fuskantar cin zarafi daga jami'an tsaro.

https://p.dw.com/p/3eOtz
Schweiz Genf | UN-Hochkommissarin |  Michelle Bachelet
Hoto: Getty Images/AFP/F. Coffrini

Akalla fararen hulla 580 ne suka gamu da ajalinsu daga farkon watan Janairun wannan shekara zuwa yanzu sakamakon rikice-rikicen kabilanci ko azabtarwa daga jami'an tsaro, a yankin tsakiyar kasar Mali mai fama da hare-haren kungiyoyin masu tayar da kayar baya.

A cikin wata sanarwar da ta fitar a yau din nan babbar sakatariyar hukumar kare hakin bil'Adama ta Majalisar Dinkin Duniya Michelle Bachelet, ta bayyana cewa ya zama tilas hukumomin kasar ta Mali su kaddamar da wani gagarumin bincike na adalci kan batun, kana kuma su hukunta duk wasu shafafu da mai da ake ganin na da hannu cikin badakalar ta kisan jama'a.

Babbar sakatariyar hukumar kare hakin bil'Adamar ta ce jama'a na bukatar shari'a ta gaskiya da biyan kudaden diya.