1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mali: Kalubalen tsaro a birnin Timbuktu

Abdourahamane Hassane AS
April 24, 2018

Wasu bangarorin Mali na cigaba da fuskantar tashin hankali inda a makon jiya aka yi harbe-harbe a filin saukar jiragen sama birnin Timbuktu kana a jiya aka harba wasu rokoki a kan sansanin sojin kasar da na MINUSCA.

https://p.dw.com/p/2wYzS
Mogadischu Somalia Autobombe Explosion Feuer Bombe
Hoto: Reuters

Wadanan hare-hare dai da ake kyautta zaton mayakan 'yan tawaye ne suka kai su, na zuwa ne kwanaki kadan bayan hare-haren da wasu 'yan bindiga suka ai a sansanin sojijin Faransa na Barkhane da ku ma rundunar MINUSMA jim kadan bayan sanarwa da ruduna sojojin Malin ta bayyana cewar ta kashe 'yan ta'adda 15 a yankin tsakiyya na kasar a makon jiya. A hirar da DW ta yi da wani dan jaridar Baba Hamdi Toure ya ce jama'a na cikin fargaba inda ya kara da cewar ''wani abu zai iya faruwa a kowane lokaci, mutane hankalinsu ba a kwace ya ke ba.''

Bayanai daga wasu majiyoyin na cewar hare-haren da aka kai a birnin Timbuktu sun fito ne daga Goundam da ke kusa da brinin na Timbuktu. Cheik Doukoure magajin garin Tele da ke cikin yankin Goundam ya ce ''ba na ganin wasu alamu da ke tabbatar da cewar wadannan hare-hare an kaisu daga nan sai ai daga wani wurin. Idan aka ce Goundam watakila daga daji ne. A yau kungiyoyin 'yan ta'adda da a 'yan tawaye sun bazu ko'ina, ya na da wahala a tantacesu''.

A shekara ta 2012 arewacin Malin ya fada cikin hannun masu kishin addini na kungiyar Al-Qaida kafin daga bisanin sojojin Faransa su koresu a shekara ta 2013 kana a sake kwato yankin arewacin Mali.