1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Boubacar Keita na neman sulhu da 'yan adawa

Binta Aliyu Zurmi MNA
June 15, 2020

Shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita na neman sulhu da abokan adawarsa da ke nemansa da ya yi murabus yana cewar a shirye yake da su hau teburin tattaunawa.

https://p.dw.com/p/3dleB
Ibrahim Boubacar Keita
Hoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Da yake jawabi a gidan talabijin mallakar gwamnatin kasar, shugaba Keita ya jaddada cewar a kullum kofarsa a bude ta ke kuma hannayensa a mike suke ga duk wanda ke bukata. Shugaban ya kara da cewar a shirye yake ya gana da 'yan jam'iyyun adawa. 

A farkon wannan watan ne dubban 'yan kasar ta Mali suka gudanar da gangami a babban birnin kasar Bamako biyo bayan wasu da aka sha gudanarwa a watan da ya gabata bayan an gudanar da zaben majalisar dokoki da ya bai wa shugaban nasara.

Jami'an Majalisar Dinkin Duniya na kungiyar tarayyar Afirka, AU da ma na kasashen yammacin Afrika sun gana da shugaba Boubakar Keita da madugun adawa Mahmoud Dicko.