1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

IBK da Cisse za su kara a zagaye na biyu

Gazali Abdou Tasawa MNA
August 8, 2018

Kotun tsarin mulkin kasar Mali ta tabbatar da cewa za a fafata a zagaye na biyu na zaben shugaban kasa tsakanin IBK da kuma Soumaila Cisse.

https://p.dw.com/p/32rEC
Mali Wahl Bildkombo | Ibrahim Boubacar Keita & Soumaila Cisse

Kotun tsarin mulkin kasar Mali ta tabbatar a wannan Laraba da Ibrahim Boubakar Keita shugaban kasar mai ci da kuma madugun 'yan adawar kasar Soumaila Cisse a matsayin 'yan takarar da za su fafata da juna a zagaye na biyu na zaben shugaban kasar na ranar 12 ga wannan wata na Agusta. 

Kammalallen sakamakon zaben da shugabar kotun tsarin mulkin kasar ta Mali Manassa Danioko ta wallafa a wannan rana ya tabbatar da cewa Shugaba IBK ne a sahun gaban zaben na ranar 29 ga watan Yuli da kaso 41,68% na kuri'un da aka kada a yayin da Soumaila Cisse ke bi masa da kaso 17,78%. 

A baya dai 'yan adawar kasar ta Mali sun yi barazanar kaurace wa zaben zagaye na biyu matsawar ba a sake kididdigar kuri'un zaben zagayen na farko ba, da ma sauke minisatan kula da harkokin zaben kasar daga kan mukaminsa. Ya zuwa yanzu dai 'yan adawar kasar ta Mali ba su kai ga cewa uffan ba a game da wannan sakamako da kotun tsarin mulkin kasar ta fitar.