Mali: An kama tsohon firaminista Maiga | Labarai | DW | 26.08.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mali: An kama tsohon firaminista Maiga

Jami'an tsaro sun kama Tsohon Firaministan kasar Mali Soumeylou Boubeye Maiga. Maiga mai shekaru 67 ya kasance na hannun daman hambararren shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita. 

Rahotanni sun ce an kama Soumeylou Boubeye Maiga ne sakamakon wani bincike da hukumomin kasar ke yi kan almubazzaranci da dukiyar kasa.

Kamfanin dillancin labaran Faransa, AFP, ya ce an kama tsohon firaministan don ya amsa wasu tambayoyi dangane da wata almundahana da aka tafka a cinikin jirgin saman shugaban kasar Mali a 2014 lokacin da Maiga yake matsayin ministan tsaro.

A shekarar 2017 ne dai aka nada Soumeylou Boubeye Maiga a matsayin firaminista kafin shekara ta 2019 lokacin da ya yi murabus bayan wasu kashe-kashe da aka yi kasar ta Mali.