Mali: An kama bindigodi a jami′ar Bamako | Labarai | DW | 21.12.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mali: An kama bindigodi a jami'ar Bamako

A Mali 'yan sanda sun kama wasu dalibai 16 da tarin makamai da suka hada da bingigogi a jami'ar Bamako babban birnin kasar a lokacin wani samame da 'yan sandan suka kai jami'ar biyo bayan wani fada.

Rikicin dai ya samo tushe ne daga zaben magatakardan kungiyar daliban sashen ilimin kimiya da fasaha na jami'ar. A cikin wata sanarwa da ta fitar a wannan Alhamis din ma'aikatar ministan tsaro na kasar ta Mali ta ce dalibin da ya rasu, ya gamu da ajalin nasa ne a sakamakon harbin bindiga. Daga cikin makaman da 'yan sanda suka kama a jami'ar baya ga daliban 16, sun hada da kananan bindigogi masu sarrafa kansu kirar gargajiya guda 20 da harsashai 19 da adduna 63d da wukake 208 da sanduna shida.