1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Imam Mahmoud Dicko ya janye zanga-zanga

Ramatu Garba Baba
July 16, 2020

Imam Mahmoud Dicko ya sanar da janye gagarumin gangamin da aka shirya gudanarwa a gobe Juma'a, maimakon hakan za a gudanar da addu'oi ga wadanda suka rasa rayukansu a yayin rikicin neman sauyin gwamnati.

https://p.dw.com/p/3fONn
Mali Imam Mahmoud Dicko
Hoto: Getty Images/AFP/H. Kouyate

Jagoran zanga-zangar kasar Mali Imam Mahmoud Dicko ya janye gagarumin gangamin da aka shirya gudanarwa a gobe Juma'a, maimakon hakan za a gudanar da addu'oi da kuma nuna alhini ga wadanda suka rasa rayukansu a yayin zanga-zangar neman sauyin gwamnati a makon da ya gabata, mutum goma sha daya ne suka mutu wasu fiye da dari suka raunata a rikicin na kwanaki uku.

Bayan sanarwar da mai magana da yawun malamin mai karfin fada a ji a kasar ya fitar a jiya Laraba,na soke zanga-zangar ya kwantar da hankulan jama'a da ke zaman dar-dar bisa fargabar barkewar rikici. Wasu kuwa, na danganta matakin Dickon, da wata ziyara da tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya kai kasar da zummar shiga tsakani don samar da maslaha.

Zarge-zarge dai, na cin hanci da rashawa da nuna halin ko in kula a rigingimun da suka lakume dubban rayuka na daga cikin batutuwan da suka harzuka jama'a wajen tilastawa Shugaba Keita yin murabus bayan shafe sama da shekaru takwas.