Mali a kan turbar demokradiyya
September 19, 2013Kasar Mali ta kasance abin koyi ta fannin siyasa da tattalin arziki ga sauran kasashen yammacin Afirka. Amma tun bayan dagulewar harkokin siyasar kasar cikin shekara ta 2012, kasar ta tsunduma cikin rikicin Abzinawa 'yan tawaye, da ya kai ga kifar da zababbiyar gwamnatin farar hula a cikin watan Maris na shekarar 2012. Yanzu lamura sun fara daidaita, inda a ranar Alhamis aka yi bikin kaddamar da sabon shugaban kasa. Shin ina ake ganin kasar ta dosa?
Manyan baki a birnin Bamako
A wannan Alhamis a birnin Bamako aka yi bikin rantsar da sabon Shugaban kasar ta Mali, Ibrahim Boubacar Keita, wanda aka rantsar tun ranar 4 ga wannan wata na Satumba. Shugaban kasar Faransa Francois Holland da sauran shugabannin Afirka da suka hada da Alassane Ouattara na Cote d'Ivoire da Sarkin Maroko Mohammed VI na cikin manyan bakin da ke halartar bikin.
Daya daga cikin muhimman batutuwa da sabon shugaban Mali Boubakar Keita zai saka a gaba sun hada da rikicin arewacin kasar, na 'yan tawayen Abzinawa da ya janyo sojoji suka kifar da gwamnatin cikin watan Maris na shekarar da ta gabata ta 2012.
Henner Papendieck na Gidauniyar GIZ ta Jamus, masani ne, wanda ya shafe shekaru yana aiki bisa shirin tallafa wa manoma da inganta harkokin kasuwanci. Inda ya ce ba daukacin al'ummar kasar 'yan tawayen ke magana da yawunsu ba:
"Ba sa wakiltar daukacin al'ummar kasar. Abin da ya dace shi ne dawo da 'yan gudun hijira domin sanin matsayinsu kan makomar kasar."
'Yan tawaye na da nasu shakkun
'Yan tawayen arewacin kasar ta Mali na kungiyar MNLA, wadanda suka kwashe shekaru suna gwagwarmayar neman kafa kasar Azawad, sun fahimci cewa amfani da karfi ba zai taba zama mafita ba. Kakakin kungiyar a kasashen Turai Moussa Ag Assarid ya bayyana babban burinsu na gaba yana mai cewa:
"Ba ma adawa da matakin saka kungiyoyin fararen hula cikin shirin tattaunawa. Abin da ba ma bukatar ya sake faruwa shi ne, tattara duk karfi ga gwamnatin tsakiya kamar yadda ya faru a shekarar 1992."
Dubban 'yan gudun hijirar kasar ta Mali da ke kasashen ketare, suna cikin masu tofa albarkacin bakinsu kan makomar kasar. Nina Wallet Intalou tana cikin wadanda suka tsere zuwa kasar Mauritaniya, ta yi nuni da cewa:
"Mahukuntan birnin Bamako ba sa mutunta yarjejeniyar tsagaita wuta. Ba su saki fursunoni ba, kuma suna kame manoma da sauran al'umma babu kakkautawa."
Dakarun Faransa sun taka muhimmiyar rawa wajen magance rikicin kasar ta Mali. Kuma bayan bikin kaddamar da sabon Shugaba Ibrahim Boubakar Keita ake wa lakabi da IBK, a wannan Alhamis, sabon shugaban yana da jan aikin mayar da martabar kasar tsakanin sauran kasashen duniya, da dinke barakar da aka samu tsakanin 'yan kasa.
Mawallafa: Dirke Köpp / Suleiman Babayo
Edita: Mohammad Nasiru Awal