1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Malesiya: Najib Razak na fiskantar sabuwar tuhuma

Yusuf Bala Nayaya
August 8, 2018

Tsohon firaminista a kasar Malesiya Najib Razak a wannan rana ta Laraba da ya bayyana a gaban kuliya ya bayyana cewa ba shi da masaniya kan sabon zargin da ake masa na hannu a badakalar cin hanci da rashawa.

https://p.dw.com/p/32nA6
Malaysia | Ex-Premier Najib Razak festgenommen
Hoto: Reuters/L. S. Sin

Ana dai zargin tsohon Firaminista Najib Razak da karkatar da Ringgit miliyan 42 wato kimanin Dala miliyan 10 inda aka zuba kudin a asusun ajiyarsa na bankin SRC International.

Najib, da ya zama firaminista tun daga 2009 har zuwa watan Mayu na wannan shekara ya zamo sha kallo a fagen bincike. Dama dai ana zarginsa da tafiyar da kudi Dala miliyan dubu hudu da dari biyar ta hanyar da ba ta dace ba ciki har da kusan Dala miliyan 700 da ake zargin an sa a asusun ajiyarsa. Wannan tuhuma ta bayan nan dai ta sa yawan tuhumar da ake wa Najib ta kai bakwai. Idan aka same shi da laifi zai kwashe shekaru 15 a gidan kaso, baya ga tara ta ninki biyar na adadin kudaden da ake zargin an sa a asusun nasa.