1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutharika ya lashe zaben shugaban kasa a Malawi

Gazali Abdou Tasawa
May 27, 2019

Hukumar zaben kasar Malawi ta bayyana a wannan Litinin shugaba mai barin gado Peter Mutharika a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa na ranar 21 ga wannan wata na Mayu.

https://p.dw.com/p/3JFXH
Schottland | Präsident von Malawi Peter Mutharika zu Besuch in Edinburgh
Hoto: picture-alliance/dpa/empics/PA Wire/Scottish Daily/F. Bremner

Hukumar zaben kasar Malawi ta bayyana a wannan Litinin shugaba mai barin gado Peter Mutharika a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa na ranar 21 ga wannan wata na Mayu inda ta ce ya samu sama da kaso 38,57 a yayin da abokin hamayyarsa M Chakwera ya samu kasa da kaso 35,41 cikin dari kana Saulo Chilima na jam'iyyar MEC kana mataimakin shugaban kasar ya zo a matsayin na uku da sama da kaso 20 cikin dari na kuri'un da aka kada

Tun a ranar Asabar da ta gabata ce dai Hukumar Zaben ta so bayyana sakamakon, amma kotun kolin kasar ta umarce ta da ta dakata har sai ta yi nazarin kalubalantar sakamakon da Chakwera ya yi a gabanta yana mai zargin gwamnati mai ci da tafka magudi da kuma tarin kura-kurai a zaben.

 Hukumar zaben ta bayyana sakamakon ne wanda da ma kungiyoyin masu sa ido na kasa da kasa da suka hada da na Turai suka bayyana a matsayin sahihi, 'yan awoyi kalilan bayan da kotun kolin kasar ta ba da izinin fitar da shi.