Makomar masallatai 150 a Tunisiya | Labarai | DW | 13.03.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Makomar masallatai 150 a Tunisiya

Tunisiya ta fara aiwatar da sabon shirin mayar da daukacin masallatan kasar a karkashin kulawar gwamnati.

Hukumomin Tunisiya na kokarin karbe ragamar tafiyar da harkokin wasu daga cikin masallatan kasar, wadanda suka ce sun kasance maboyar masu tsattsauran ra'ayi ne, tun bayan juyin juya halin da ya afku a kasar a shekara ta 2011. Wannan matakin dai ya biyo bayan murabus din gwamnatin da ke karkashin jagorancin jam'iyyar Ennahda, wadda ke da ra'ayin bin dokokin Musulunci, wadda wasu ke yi wa suka bisa gaza shawo kan matsalar masu tada rigingimu - da sunan addini.

Matsalar dai ta kunno kai ne tun bayan da mayakan sa kai suka ci gajiyar da ke tattare da juyin juya halin da ya afku a wasu kasashen Larabawa da kuma na arewacin Afirka. A cewar Abdessattar Badr, wani babban jami'i a ma'aikatar kula da harkokin addini ta kasar Tunisiya, kimanin makonni biyu da suka gabata ne, gwamnati ta fara aiwatar da tsarin, wanda kuma take fatan kammalawa cikin tsukin watanni uku. Daga cikin masallatai 5,100 da ke Tunisiya dai, 150 ba sa karkashin kulawar gwamnati, inda wasu kimanin 50 kuma ke karkashin ikon masu tsattsauran ra'ayin addini.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Mohammad Nasiru Awal