Makomar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya | Labarai | DW | 17.01.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Makomar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa zubar da jinin da ake yi a rikicin addini da ake fama da shi a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ka iya komawa yakin kisan kiyashi .

Wannan gargadi dai ya biyo bayan ci gaba da gwabza fadaa kasar a dai dai lokacin da 'yan majalisun dokoki ke kokarin zabar sabon shugab a Jamhuriyar Afirka ta TSakiyar. Yaki da tashe-tashen hankula dai ya ci gaba da wanzuwa a kasar, duk kuwa da cewa a makon da ya gabata tsohon shugaban kasar Michel Djotodia ya sauka daga mukaminsa, bayan da ya fuskanci matsin lamba daga shugabannin kasashen yankin tsakiyar Afirkan.

Rahotanni sun bayyana cewa a kallah mutane bakwaine aka hallaka a baya-bayan nan, wanda hakan ya sanya daraktan kula da ayyukan bada agaji na Majalisar Dinkin Duniya John Ging ya shaidawa manema labarai cewa alamu duka sun bayyana na irin yadda salon yakin kasashe kamar Ruwanda da Bosniya ya kasance a kazamin rikicin addinin da Jamhuriyar Afirka ta TSakiyar ke fama da shi.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Usman Shehu Usman