Makomar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya bayan murabus na Djotodia | Siyasa | DW | 11.01.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Makomar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya bayan murabus na Djotodia

Ana ci gaba da samun rikici a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya duk da murabus din da gwamnatin wucin gadin kasar tayi.

Kwararru a harkokin da suka shafi yankin tsakiyar Afirka sun bayyana samar da gwamnatin wucin gadin da za ta kunshi daukacin sassan da ke da hannu a cikin rikicin Jamuriyar Afirka ta Tsakiya a matsayin hanyar samar da kyakkyawar makoma ga kasar, bayan murabus din da shugaban wucin gadin kasar Michel Djotodia yayi a wannan jumma'ar.

Duk da murabus din da shugaban wucin gadin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya Michel Djotodia ya yi tare da Fira ministan kasar Nicolas Tiangaye bisa matsin lambar al'ummomin kasa da kasa, an ci gaba da samun rigingimu a kasar bayan sanarwar, inda kuma dakarun Faransa da na Kungiyar Tarayyar Afirka da ke aikin wanzar da zaman lafiya a kasar, suka yi ta harbi a iska domin kwantar da hankulan jama'a, yayin da bata gari ke kai hare hare akan shagunan mabiya addinin Musulunci da kuma masallatai. Sai dai kuma akwai wuraren da rikicin ya janyo mutuwar jama'a musamman a Bangui, babban birnin kasar.

Matsayin mazauna Bangui ga murabus na Djotodia

Tunda farko dai, akwai wadanda suka yi marhabin da murabus din da Djotodia ya ayyana yayin taron kungiyar kasashen yankin tsakiyar Afirka da ya gudana a birnin Ndjamena na kasar Chadi, karkashin jagorancin shugaban Chadi Idriss Deby Itno, wanda kuma ke shugabantar kungiyar kasashen yankin.

Wa'adin makonni biyu ne dai Kungiyar ci gaban tattalin arzikin Kasashen Tsakiyar Afirka ta debawa majalisar dokokin wucin gadin kasar a karkashin jagorancin Alexandre-Ferdinand Nguendet domin zaban mutumin da zai jagoraci gwamnatin wucin gadin da za ta maye gurbin Djotodia da tsohon fira ministansa Tiangaye, wadda kuma Thierry Vircoulon, darektan kula da harkokin yankin tsakiyar Afirka a Kungiyar Warware Rigingimu ta Kasa da Kasa, wato International Crisis Group da ke Nairobin kasar Kenya ya shaidawa DW cewar, tilas ne gwamnatin ta kunshi kowa da kowa:

Ya ce " Ina ganin za mu wayi gari ne mu ga an samar da gwamnatin wucin gadin da za ta kunshi daukacin masu ruwa da tsaki a cikin rikicin na Jamhuriyyar Afirka ta Tsakiya, wadda za ta hada da wakilan kungiyar 'yan tawayen Seleka da kuma ta Anti Balaka."

Zentralafrikanische Republik Michel Djotodia Tschad Idriss Deby

Djotodia(dama) da shugaba Idriss Deby na Chadi

Bangarorin da ke kan gaba wajen warware rikicin

Thierry Vircoulon, ya kuma kara da cewar, abin da ya fito fili dangane da kokarin warware rikicin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya dai, shi ne cewar, kungiyar kasashen yankin, suna daukar dukkan matakan da suka wajaba kuma - a siyasance, domin tinkarar matsalar da suke ganin ta shafesu ne, inda ya bada misali da cewar, ai taron shugabannin kasashen yankin tsakiyar Afirka ne ya sahhalewa hatta shi kansa Djotodia kasancewa shugaban wucin gadi, kamin nemanshi da yin murabus a yanzu:

Ya ce " Kungiyar ci gaban tattalin arzikin Kasashen Tsakiyar Afirka ta taka rawa, kamar yadda ita ma Chadi da ke jagorantar kungiyar ta taka rawar da ta kai ga samun wannan ci-gaba. Kasashen yankin na kaunar warware matsalar su da kansu wadda kuma ke nuna cewar, sun ajiye Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Tarayyar Afirka zuwa gefe guda kenan."

Masanin dai ya ce, samar da kyakkyawar makoma ga kasar dai, ya dogara ne ga irin mutanen da za su zama wakilan sabuwar gwamnatin wucin gadin da za ta tafiyar da lamura a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, a dai dai lokacin da wasu ke hasashen yiwuwar fitowarsu daga shugabannin addini da na al'umma maimakon kyale batun a hannun 'yan siyasa kadai.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Suleiman Babayo

Sauti da bidiyo akan labarin