Makomar Afurka | Siyasa | DW | 24.02.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Makomar Afurka

Take-taken kasashen Afurka wajen shawo kan rikicin Togo ka iya zama mizani a game da alkiblar da nahiyar zata fuskanta nan gaba

Rikicin siyasar da ya kunno kai a kasar Togo dangane da wanda zai gaji marigayi Gnassingbe Eyadema da kuma murabus din da John Githongo yayi daga mukaminsa na shugaban hukumar yaki da cin hanci a kasar Kenya abubuwa ne dake barazanar mayar da murna ciki dangane da makomar al’amuran nahiyar Afurka. Wadannan matsalolin guda biyu ka iya gurgunta manufofin kungiyar tarayyar Afurka ta AU, tun kafin su dauki wani tsayayyen fasali, musamman ganin yadda kungiyar ke ci gaba da lalube a cikin dufu wajen neman bakin zaren warware matsalolin tsaro a Darfur da Zimbabwe. Canjin mulkin da aka yi a cikin ruwan sanyi a kasar Kenya a shekara ta 2002 ya ba wa jama’a kwarin guiwa a kasar ta gabacin Afurka a game da rungumar demokradiyya tsantsa da gusar da cin hanci da farfadowar tattalin arzikinta. Takanas ta Kano shugaban gwamnatin Jamus da ministar taimakon raya kasashe masu tasowa ta kasar suka kai wa Kenya ziyara domin girmama wannan kyakkyawan ci gaba da ta samu. Amma fa ba a dade ba murna ta sake komawa ciki. A can kasar Togo ma mutane sun dokata wajen ganin canje-canjen manufofi ya samu a kasar tasu bayan shekara da shekaru na danniya da kama-karya. Kungiyar tarayyar Turai tayi matsin lamba tayi matsin lamba har sai da aka cika alkawarin gudanar da zabe da aiwatar da garambawul ga siyasar kasar ta yammacin Afurka. Amma fa matakan ta mahukuntan kasar suka dauka na yi wa daftarin tsarin mulkinta surkule domin ba wa dan marigayi shugaba Gnassingbe Eyadema damar gadon kujerar mulkin daga mahaifinsa abu ne dake neman sake mayar da hannun agogo baya da durmuya kasar cikin mulki na kama karya da fir’aunanci. Warware wadannan matsaloli guda biyu shi ne zai zama mizanin makomar nahiyar Afurka baki daya. Muddin kungiyar tarayyar Afurka ta AU da kungiyar ta da komadar tattalin arzikin nahiyar ta NEPAD da gaske suke a game da sabuwar alkiblar da siyasar nahiyar ta fuskanta to kuwa wajibi ne su dauki tsayayyun matakai. In kuwa ba haka ba to kuwa duk wata lasar takobi da suke magana ce ta fatar baki kawai. Kuma za a wayi gari nahiyar Afurka na fama da yamutsi da talauci da tashe-tashen hankula da kuma rashin sanin tabbas game da makomar rayuwar talakawanta. Kazalika irin wannan mummunan ci gaba ka iya zama gobarar titi ga ‚yan ta’adda, wadanda zasu rika amfani da nahiyar domin shirya hare-harensu na ta’addanci. Babban abin da ake bukata a yanzun shi ne kasashen Afurka su nuna halin sanin ya kamata su sake wani sabon yunkurin wajen tinkarar matsaloli na cin hanci da rashin adalci na mahukunta da mulke-mulken danniya da kama karya. Wannan ita ce sahihiyar alkiblar da ya wajaba su fuskanta ba zabi.