Majalisar Yukren ta amince da kafa gwamnatin kawance | Labarai | DW | 27.02.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Majalisar Yukren ta amince da kafa gwamnatin kawance

An zabi Yatseniuk a matsayin Firaminista da zai jagoranci gwamnati. Sai dai ana ci gaba da rikici musamman a yankin Krimea da ke gabar tekun Bahar Aswad.

A wannan Alhamis majalisar dokokin Yukren ta amince wata gwamnatin kawance ta jagoranci kasar kana ta ba da shawara tsohon ministan tattalin arziki Arseny Yatseniuk ya shugabanceta a matsayin Firaminista. Bayan zabansa Yatseniuk ya fada wa majalisar dokokin cewa kasar na dab da fadawa cikin rikicin tattalin arziki da na siyasa, sannan ya yi gargadin cewa Yukren na fuskantar barazana kan kasancewarta kasa daya. Ya yi alkawarin ci gaba da bin manufar kusanci da tarayyar Turai.

A kuma can yankin tsibirin Krimea mai rinjaye mazauna masu magana da harshen Rashanci, mutane kusan 30 dauke da muggan makamai sun mamaye ginin majalisar dokoki da na gwamnatin yankin dake Simferopol hedkwatar tsibirin dake a tekun Bahar Asawad. Mutanen sun bayyana kansu a matsayin masu kare al'ummar yankin na Krimea. Yanzu haka dai jami'a tsaro sun yi wa ginin kawanya.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Zainab Mohammed Abubakar