Majalisar Italiya ta sallami Berlusconi | Labarai | DW | 27.11.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Majalisar Italiya ta sallami Berlusconi

Silvio Berlusconi ya rasa kujerarsa a majalisar dattawan Italiya. Wannan mataki na iya kawo ƙarshen rawar da ya dade ya na takawa a fagen siyasar ƙasar

Former Prime Minister and leader of Forza Italia, Silvio Berlusconi listens to Italys' Prime Minister Enrico Letta's speech on October 2, 2013 at the Senate in Rome before today's confidence vote at the Parliament. Enrico Letta warned lawmakers ahead of a crucial vote of confidence today that the country ran a 'fatal' risk as Silvio Berlusconi tries to topple his government. 'Italy runs a risk that could be a fatal risk. Seizing this moment or not depends on us, on a yes or a no,' Letta said in his address. AFP PHOTO / FILIPPO MONTEFORTE (Photo credit should read FILIPPO MONTEFORTE/AFP/Getty Images)

Silvio Berlusconi niedergeschlagen

Bayan da kotu ta same shi da laifin yin rufa-rufa kan kuɗin haraji, majalisar dattawan ƙasar Italiya ta kori Silvio Berlusconi, tsohon Firaministan ƙasar daga zaurenta. Shugaban majalisa ne da kansa ya faɗawa Berlusconi cewa, daga yanzu ba shi da kujera a majalisar, abinda ke nufin an salla me shi kenan.

Magoya bayan jam'iyar Berlusconi da ke cikin majalisar dai sun yi iya ƙoƙarinsu na hana wannan korar-kare da aka yi wa fitaccen dan siyasa kana hamshaƙin mai kuɗi a ƙasar Italiya. A watan Augusta kotu ta ɗaure Silvio Berlusconi na tsawon shekaru huɗu a gidan yari, bayan da aka same shi da laifin yin coge wajen biyan kuɗin harajin wani kamfaninsa na yaɗa labarai.

Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe