1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Muhawara kan dokar gina wuraren ibada a Nijar

Salissou Boukari AMA
June 17, 2019

Gwamnati a Jamhuriyar Nijar ta shigar da wani kudirin doka a gaban majalisar dokoki don tsara yadda za a dinga tafiyar da ayyukan addinai, tare da kawo sabon tsari a gina masallatai da sauran wurare ibadun jama'a.

https://p.dw.com/p/3KbWE
Niger Anti Charlie Hebdo Protest Islam Koran 17.01.2015
Hoto: Reuters/T.Djibo

Majalisar dokokin Jamhuriya Nijar ta tafka muhawara kan dokar kan tsara harkokin adinai wacce ta janyo cece-ku-ce a fadin kasar daga kungiyoyin adinin Muslunci, wadanda a can baya suka nuna rashin amincewarsu game da dokar, tare da jan hankalin majalisar ta dokoki da ta guji sanya hannu kan kudurin dokar da gwamnati ta gabatar a gabanta

Kwanaki biyu kafin zaman majalisar dokoki kan dokar, wasu kungiyoyin malaman addinin Musulunci takwas (8) sun kira wani taron wa’azi domin sanar da al’umma irin abubuwan da dokar ta kunsa tare kira ga hukukomi da su yi hatsi da ita kamar yadda Ustaz Chaibou Salma Limamin masallacin juma’a na unguwar garbado a birnin Niamey ya shedawa manema labarai.

Tuni majalisar dokokin kasar ta soma aikin duba dokar duk da korafe-korafen da bangarorin addinai suka yi musamman ma malamai tana mai cewa ba tun yanzu aka soma shirye-shiryen tsara dokar ba, domin kuwa kwamitin ‘yan majalisa da ke kula da wannan batu ya tattauna da babbar majalisar malaman adinin Muslunci ta kasa da ta kumshi kungiyoyin adinin Muslunci da dama, kana kuma mafi yawa sun amince da wannan tsari.

Ra’ayoyi dai sun bambanta tsakanin ‘yan majalisar dokokin na Jamhuriyar Nijar da ke tattauna wannan batu, inda yayin da wasu ke cewa a amince da dokar wasu kuma na cewa a yi hatsi da ita ko da yake da dama sun yi kira da a kaucewa irin abubuwan da suka wakana a birnin Maradi a karshen makon jiya inda matasa suka yi kone-kone dangane da kama wani malami da yayi wa'azi kan dokar.