1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afirka ta Kudu an sake zaben Cyril  Ramsphosa

Abdourahamane Hassane
May 22, 2019

'Yan majalisar dokoki a Afirka ta Kudu sun sake zaben Cyril  Ramsphosa a matsayin shugaban kasa bayan da jam'iyarsa ta ANC ta samu nasara a zaben da aka gudanar a farkon wannan wata na Mayu.

https://p.dw.com/p/3IvG6
Südafrika Präsident Cyril Ramaphosa
Hoto: AFP/M. Spatari

 Cyril Ramaphosa wanda aka sake zaba ba da wani mamaki ba, an shirya cikin kwanaki na gaba zai bayyana sunayen sabbin manbobin majalisar minitocin gwamnatinsa. Wace ke da jan aiki a gabanta na yaki da cin hanci a karbar rashawa tare da sake farfado da tattalin arzikin kasar ta Afirka  ta Kudu da ke tafe tanga-tangal.