Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah wadai da kisan jami′inta a Mali | Labarai | DW | 15.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah wadai da kisan jami'inta a Mali

Mayakan sakai a arewacin Mali na amfani da sabon salon binne bama-bamai a kan hanya a arewacin kasar da ta sha Fama da rikicin masu tada kayar baya.

Wani jami'i da ke aikin wanzar da zaman lafiya daga kasar Chadi ya mutu, wasu hudu kuma suka jikkata bayan da motar da ke dauke da su ta taka wani bam da aka binne a arewacin Mali kamar yadda jami'ai suka bayyana.

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki Moon ya yi Allah wadai da wannan mugun aiki. Wani jami'i da ke aikin da rundunar wanzar da zaman lafiya ta MUNISMA ya fada wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa sun rasa mutum daya bayan da motar su ta ci karo da abin fashewa da aka binne a yankin Aguelhoc.

A cewar mai magana da yawun sakataren Majalisar Dinkin Duniya wannan hari da ya yi sanadin mutuwar mutum daya da raunata wasu karin mutane hudu, ba zai kawo cikas ba a kokarin da majalisar ke yi na ganin an samar da zaman lafiya a wannan kasa ta Mali.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Suleiman Babayo