Majalisar Dinkin Duniya ta ce ana samun nasara a yaki da Aids ko Sida | Labarai | DW | 20.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Majalisar Dinkin Duniya ta ce ana samun nasara a yaki da Aids ko Sida

A cikin shekaru kimanin 10 yawan mutanen da cutar mai karya garkuwar jiki ta yi ajalinsu ya ragu matuka.

Symbolbild Aids Medikament (picture-alliance/dpa/J. Kalaene)

Irin yawan magungunan da masu cutar Aids ke sha ke nan

Yawan mutanen da ke mutuwa sakamakon cutar Aids ko Sida ya ragu da kusan kashi 50 cikin 100 a tsukin shekaru 10 da suka gabata. A cikin wani rahoto da ta wallafa hukumar Majalisar Dinkin Duniya mai kula da cutar Aids wato UNAIDS, ta ce a bara mutane miliyan daya suka mutu sakamakon kamuwa da cutar mai karya garkuwar jiki. A daidai wannan lokaci kuma yawan sabbin masu kamuwa da kwayoyin cutar ya ragu da mutum miliyan 1.8, sannan a lokaci guda an samu karuwar yawan wadanda ake wa jinya da magungunan HIV. Rahoton ya nuna cewa a shekarar 2016 mutane miliyan 19.5 daga cikin mliyan 36.7 aka yi wa jinya da magungunan na HIV, abin da ke zama na farko wajen samun fiye da kashi 50 cikin 100 na masu dauke da cutar da aka yi wa magani.