Majalisar Dinkin Duniya ta amince da ɗaukar matakin soja a Mali
December 21, 2012
Komitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, ya kaɗa ƙuri'ar amincewa da matakin soji a arewacin Mali domin ƙwato yankin da ya faɗa a hannun ƙungiyoyin kishin islaman da suka haɗa da Ansar Dine da Mujao da kuma Aqmi wato Alqa'ida a yankin Maghreb. Dama tun can baya an samu rashin jittuwa tsakanin membobin komitin, musamman Faransa da Amurka a kan batun.
To saidai ko yanzu akwai sauran lokaci, inji wani jami'in diplomasiya,wanda ya ce ko da rundunar ta ECOWAS za ta fara aikinta na 'yantar da yankin sai da nan zuwa watan Satumban shekara ta 2013. Ita dai ECOWAS ta ce sojojinta da suka kai kimanin 3.300,na cikin shirin ko-ta-kwana ga isa yankin na arewacin Mali.
A nashi ɓangare, sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-Moon,ya ce babu dole sai rai ya so ga ƙasashen duniya a gudunmuwar da za su iya badawa a maimakon a ce Majalisar Dinkin Duniya ce zata ɗauki ɗawainiyar dakarun.
Mawallafi: Issuhu Maman
Edita: Yahouza Sadissou Madobi