Majalisar dattawan Najeriya ta ce da sakel a yaƙi da ta'addanci
March 21, 2013A wani abun dake zaman kama hanyar gwada kwanji a tsakanin fadar gwamnatin kasar da yan majalisar Tarrayar a kan batun yakin da ta'addancin kasar dake cikin shekarar sa ta uku, majalisar dattawan kasar ta nemi sauyin taku a bangaren gwamnatin da ta bada kudi amma kuma wankin hula ke neman kai ta dare
An dai ga kisan dubban milliyoyin Nairori an kuma share dare da farmaki iri-iri, to sai dai kuma daga dukkan alamu tana shirin zaman an kasa ga gwamnatin da a karon farko ke fuskantar dawowa daga rakiyar gwamnatin kasar a cikin yakin da ta'adancin ta a bangaren majalisar dattawan kasar.
Majalisar dattawan kasar dai tace lokaci ya yi na mantawa da batun karfin tuwo da nufin kawo karshen matsalar dake cikin shekarar ta ta uku da kuma ta kai ga lamushe rayukan yan kasar da dama.
Yan majalisar da suka zauna suka yi nazari da karatu irin na ta natsu dai, sun ce daga hakarkari da na isa kan batun karfin tuwo ga yakin dai batu ne da ya kamaci zama tarihi a bangaren mahukuntan kasar da suka zauna suka kalli karuwar tashin boma bomai ba adadi a cikin dan kankanin lokaci.
Sabon martanin majalisar da ya zo kasa da yan kwanaki da harin da ya hallaka mutane da dama a birnin Kanon Dabo, sannan kuma ya sake tada tsohon mikin matsalar dai daga dukkan alamu na iya bude sabon babin rikici a tsakanin fadar gwamnatin da shugaban ta yace basu da niyyar yin ahuwa ga fatalwa da kuma yan majlisar da suke cewar karatun nasa bai zo daidai da tunani irin na shugabanni ba. Abun kuma da a cewar Senator Kabiru Gaya dake zaman dan majalisar dattawa daga jihar Kano ya sanya sauko wa daga dokin nakin zama wajibi.
Zaman lafiya a cikin kasa ko kuma ci gaba a cikin asarar rayuka dai, ko bayan matsin lambar cikin gidan kasar ta Najeriya dai, gwamantin har ila yau na fuskantar sabuwar annobar satar baki yan kasashen wajen da daga dukkan alamu ta kama hanyar kara jefa fadar ta Aso Rock cikin tsaka mai wuya.
Shugaban kasar ta Najeriya dai alal misali ya share tsawon mako na jiya yana bada tabbaci na kariya dama ceto bakin a idanun shugabannin dake kai kawo cikin kasar da nufin neman mafitar matsalar.
To sai dai kuma a cewar Dr Doyin Okupe dake zaman mashawarcin shugaban kan harkokin jama'a duk wani kokari na kushe gwamnatin na zaman batu na rashin sanin al'amura.
"Wadanda suke irin wadannan kalamai basu da masaniyar abun da ake nufi da yaki da ta'addanci cikin kasa. Matsala ce babba musamman ma inda yan ta'addan ke zaman na cikin gida kamar Boko Haram".
Abun jira a gani dai na zaman mataki na gaba cikin rikicin da ya fyadi sarki sannan kuma ya kai ga rauni ga ruhi dama arzikin talakan cikin kasar ta Najeriya.
Mawallafi: Ubale Musa
Edita: Usman Shehu Usman