Majalisar dattawa ta Amirka ta amince da dokar baƙi
June 28, 2013Talla
Majalisar wace yan jam'iyyar Demokrat ta Barack Obama ke da rinjaye a cikinta, ta kaɗa ƙuri'a 68 yayin da 32 na republicain suka hau kujerar naƙi. Kuma daga cikin 'yan majalisar na addawa na Republican guda 14 ne suka kaɗa ƙuri'ar amincewa da dokar. Nan gaba ne dai za a sake gabatar da dokar a gaban 'yan majalisar wakilai a mataki na biyu, wanda kuma idan ta samu karɓuwa, baƙin haure ne da dama za su samu tarkardun zama yan ƙasa da zaran sun cika shekaru 13. Yanzu haka dai akwai baƙi 'yan ƙasashen waje kamar miliyan 11 waɗanda ba su da takardun zama.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu