Majalisar CNT a Bangui ta fara zaman taronta | Labarai | DW | 14.01.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Majalisar CNT a Bangui ta fara zaman taronta

Majalissar riƙon ƙwarya ta ƙasar Jamahuriyar Afirka ta Tsakiya CNT ta fara wani zaman da a cikinsa za ta zaɓi sabon shugaban ƙasar na riƙon ƙwarya.

Majalissar riƙon ƙwarya ta ƙasar Jamahuriyar Afirka ta Tsakiya, ta soma wani zaman taro a wannan Talatar, domin zaɓen sabon shugaban ƙasar na riƙon ƙwarya bayan da shugaba Michel Djotodia ya yi murabus a ranar Jumma'a da ta gabata. Mataimakiyar kakakin majalisar Léa Koyassoum Doumta ce ke jagorantar wannan babban zaman taro sakamakon rashin kasancewar shugaban na riƙo Alexandre-Ferdinand Nguendet wanda ke jagorancin ƙasar na dan lokaci tun daga ranar Lahadin nan da ta gabata.

Majalisar riƙon ƙwarya ƙasar ta CNT, na da a kalla hurumin kwanaki 15 domin zaɓen sabon shugaban na riƙo, wanda zai canji Djotodia tare da neman mayar da doka da oda a ƙasar da ta kasance tamkar a sake, bayan murabus ɗin da Shugaban ƙasar ya yi, da firaministansan shi Nicolas Tiangaye, da ƙasashen duniya ke zargi da ƙasa taɓuka komai wajan hana kashe-kashen da ya wakana a ƙasar. Ana iya cewa al'ammura a wasu fannonin sun fara daidaituwa duk da cewar babu tabbas har yanzu cikin wannan ƙasa.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita: Umaru Aliyu