Majalisar Bundestag ta amince Jamus ta taimakawa Mali
January 31, 2013Jiya ne Majalisar Dokokin Bundestag ta yi muhawara game da tallafin da Jamus za ta baiwa Mali, a daidai lokacin da ƙasar ta shiga gwagwarmaya ƙwato yankinta na arewa, da masu tsatsauran kishin addinin Islama suka mamaye.
Tun lokacin da Faransa ta ƙaddamar da yaƙin belin arewancin ƙasar Mali ƙasashen Turai da dama suka baiyana aniyar bada haɗin kai ga Faransa domin cimma burin da a ka sa gaba.A nata ɓangare gwamnatin Jamus ta tsara nau'o' in tallafin da ta ke da burin kaiwa ƙasar Mali, da zaran ta samu haɗin kai daga Majalisar Dokokin Bundestag.
A muhaura da suka shirya jiya, 'yan majalisar Bundestag sun yanke shawara cewar babu gudu babu ja da baya, Jamus za ta shiga sahun ƙasashen duniya domin belin ƙasar Mali.Saidai sun yi na'am da cewar Jamus ba za ta shiga filin daga ba.
Za ta fi bada fifiko ga taimakon raya ƙasa da kuma bada horo da sojojin Mali.
A jawabin da ya gabatar ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle ya baiyawa wajibcin kai ɗauki ga yankin arewacin Mali kuma ya bada dalilai:
Ya ce:Arewacin Mali yanki mai fama da matsaloli da dama.Saboda haka ne ma ya ke yawan fuskantar matsaloli.Banda taimakon raya kasa domin bunƙassa tattalin arzikin yanki da kyatata rayuwar al'umarsa, za mu bada gudumawa a ƙoƙarin laluben hanyoyin warware rikicin ta hanyar siyasa.
Jamus ta yi alƙawarin ware tsabar kuɗi dallar Amurika miliya 10 zuwa 120.A yayin da ta ke tsokaci game da taimakon Jamus a Mali tsofuwar ministar taimakon raya ƙasa Heidmarie Wieczorek-Zeul ta baiyana buƙatar ganin yunƙurin ƙwatar yankin arewacin ƙasar na tafiya ƙafa da da ƙafada da shirye-shiryen zaɓe ta na cewa:A daidai lokacin da hukumomin a fadar mulki ta Bamako ke ƙoƙarin maida doka da oda yankin arewa, wajibi ne su kiyaye da kare haƙƙoƙin jama'a, sannan kuma su cigaba da shirin zaɓe, wanda zai maiyar da Mali bisa tafarkin demokraɗiya.
Game da matakin da ƙungiyar Tarayya Turai ta dauzka na tura dakarun da za su bada horo ga sojojin Mali, a cikin wata mai kamawa ne ,Majalisar Dokokin Bundestag za ta muhaura domin tantance yawan sojojin da Jamus za ta aikawa a cikin wannan tawaga.
A yayin da a ɓangare daban-daban na duniya ƙasashe ke cigaba da shiyre-shiryen bada taimakon ga ƙasar Mali sojojin Faransa da na Mali na cigaba da ƙwace biranen da ke ƙarƙashin ƙungiyoyin masu tsatsauran kishin addinin Islama ɗaya bayan ɗaya.
A jimilce su na cimma wannan nasarori ba tare da fuskantar turjiya mai tsanani ba,ko da shi a wannan Alhamis sojoji biyun na ƙasar Mali sun rasa rayuka, sakamakon tarwatsewar wata bam da motarsu ta taka, tsakanin Hombori da Douenza.
Shugaban riƙwan ƙwaryar ƙasar Mali Pr Dioucounda Traoré a cikin wata hira da kafofin sadarwa ya ce a shirye suke su hau teburin shawara da ƙungiyar tawayen MNLA domin nazarin cimma yarjejeniya,amma shugaban yayi watsi da tayin ƙungiyar MIA wadda ta ɓalle daga Ansar Dine.
Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Umaru Aliyu