1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar Amirka ta dage zaben kakakinta

Mouhamadou Awal Balarabe MAB
January 5, 2023

Rikicin da ke tsakanin 'ya'yan jam'iyyar Republican a majalisar wakilan Amirka na ci gaba da hana ruwan guda wajen zaben Kevin McCarthy a matsayin sabon kakaki.

https://p.dw.com/p/4LlnT
Yadda zaben kakaki ya gudana a majalisar wakilan AmirkaHoto: Andrew Harnik/AP Photo/picture alliance

Wasu masu ra'ayin rikau na jam'iyyar Republican sun ki goyon bayan dan takarar Kevin McCarthy, a lokacin da aka kada wani sabon zagaye na kuri'a. ‘Yan majalisar wakilan Amirka sun dage muhawarar har zuwa yau Alhamis bayan jimillar kada kuri'a sau shida a cikin kwanaki biyu ba tare da an yi nasara ba.

McCarthy shi ne wanda aka fi so ya gaji kakakin majalisar 'yar Democrat Nancy Pelosi. Sai dai jam'iyyar Republican ta dogara ne da kuri'un magoya bayan tsohon shugaban kasar Donald Trump kusan 20, wadanda suke ganin cewa Kevin McCarthy na da matsakaicin ra'ayi, saboda haka suka hana nada shi a matsayin kakakin majalisa.