Mai magana da yawun Trump ta yi murabus | Labarai | DW | 01.03.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mai magana da yawun Trump ta yi murabus

Wata mai magana da yawun shugaban kasar Amirka Hope Hicks ta sanar da yin murabus daga mukaminta, bayan da ta kamalla bayar da bahasi gaban hukumar da aka kafa kan binciken zargin Rasha a zaben shugaban kasa na 2016.

Hicks mai shekaru ashirin da tara ta fidda sanarwar bayan barin mukaminta, inda a ciki ta godewa shugaba Trump kan damar da ya ba ta na yin aiki tare da shi. Ba ta yi karin bayani kan dalilan ta na barin aikin ba sai dai ta ce ta na cike da farin ciki kan rawar da ta taka a gwamnatin da Trump ke jagoranta.

Misis Hicks ta kasance daya daga cikin wadanda suka yi aiki kut-da-kut da shugaba Donald Trump tun daga lokacin yakin neman zabe da ta kasance mai magana da yawun shugaban da kuma ba shi shawarwari ya zuwa shugabar sashen yada labarai a fadar White House.