1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zinédine Zidane zai fice daga Real de Madrid

Abdourahamane Hassane MNA
May 31, 2018

Mai horar da 'yan wasan kwallon kafa na Real Madrid na Spain Zinedine Zidane dan kasar Faransa mai asili da Aljeriya ya ce zai ajiye aikin horar da Real Madrid.

https://p.dw.com/p/2yiK6
UEFA Champions League Achtelfinale | Paris St. Germain - Real Madrid | Zinedine Zidane
Hoto: Reuters/G. Fuentes

Hakan kuwa na zuwa ne kwanaki kalilan  bayan da Real Madrid  ta samu nasara ta uku a jere  ta lashe kofin zakaru na Turai.

A wani taron manema labarai da ya yi Zidane dan shekaru 45 da haifuwa  wanda ya zo  Real Madrid a shekara ta 2016, ya ce ba zai ci gaba da horar  da 'yan wasan ba na Real Madrid a shekarr badi.

Ya zuwa yanzu dai Zizou kamar yadda ake yi masa la'akabi bai ce  ba zai sake neman wani klub din ba don ci gaba da yin aikinsa na horaswa.