Mai fafutukar ′yancin Sahrawi ya rasu | Labarai | DW | 01.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mai fafutukar 'yancin Sahrawi ya rasu

Kungiyar Polisario Front da ke fafutukar samun 'yancin cin gashin kai na yankin Sahrawi a kasar Moroko ta sanar da rasuwar shugabanta Mohamed Abdelaziz.

Jagoran fafutukar samun 'yancin cin gashin kai na yankin Saharawi Mohamed Abdelaziz

Jagoran fafutukar samun 'yancin cin gashin kai na yankin Saharawi Mohamed Abdelaziz

A wata sanarwa da kungiyar ta fitar, ta nunar da cewa Abdelaziz wanda ya dade yana fafutukar samun 'yancin cin gashin kai na yankin na Sahrawi, ya rasu ne bayan fama da rashin lafiya. Abdelaziz dai ya jagoranci kungiyar ta Polisario Front na tsahon kusan shekaru hudu. Rasuwar tasa dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da makomar yankin na Sahrawi ke cikin rashin tabbas, bayan da mahukuntan kasar Moroko suka fatattaki mafiya yawan jami'an Majalisar Dinkin Duniya da ke yankin.