Mahukuntan Italiya na daukan mataki | Labarai | DW | 21.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mahukuntan Italiya na daukan mataki

Mahukuntan Italiya na daukan mataki kan masu safarar mutane domin shiga nahiyar Turai ta barauniyar

'Yan sadan kasar Italiya sun kama matukin jirgin ruwan da ya yi hadari dauke da bakin haure kimanin 800 kusa da gaban ruwan kasar Libiya. Ministan cikin gida na kasar ta Italiya Angelino Alfano ya bayyana haka inda ya kara da cewa an kuma kama daya daga cikin masu aiki a jirgin ruwan.

Galibin mutane da suka hallaka wajen shiga nahiyar Turai sun fito ne daga kasashen Kudu da Sahara na Afirka. Mafi yawa daga Eritrea, da Somaliya, da Saliyo, da Mali, da Senegal, da Gambiya, da Cote d'Ivoire da kuma Habasha.

Shugaban kasar Congo-Brazzaville Denis Sassou Nguesso ya nemi kasashen Turai da na Afirka su yi aiki tare wajen magance matsalolin da ake samu a kasar Libiya, wanda zai taimaka a kare muce-macen da ake samu kan teku na masu neman shiga kasashen Turai ta barauniyar hanya.