Mahukunta sun haramta gangami a Kwango | Labarai | DW | 20.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mahukunta sun haramta gangami a Kwango

An dai katse hanyoyin sadarwa a birnin Brazzaville kafin fara gangamin da zai yi adawa da shirin kuri'ar raba gardama ranar Lahadi.

Kongo Präsident Denis Sassou-Nguesso

Shugaba Denis Sassou Nguesso

Mahukunta a Jamhuriyar Dimokradiyar Kwango a ranar Talatan nan sun haramta duk wani nau'i na zanga-zanga bayan da bangaren adawa suka shirya gangami na nuna kin amincewa da ci gaba da makalewa a kan mulki da shugaban kasar ke yi bayan kuwa ya zauna a wannan kujera gwamman shekaru.

An dai katse hanyoyin sadarwa a birnin Brazzaville kafin fara gangamin da zai yi adawa da shirin kuri'ar raba gardama ranar Lahadi, da za ta ba wa shugaba Denis Sassou Nguesso damar yin kwaskwarima ga kundin tsarin mulkin kasar yadda zai samu damar yin tazarce a wani sabon wa'adi na mulkin wannan kasa. Tun daga 1997 ne shugaban ke kan mulki bayan wani yakin basasa da kasar ta shiga. Tun dai a baya ma a shekarun 1979 zuwa 1992 shugaba Nguesso ya mulki wannan kasa ta Kwango.

Sa'oi dai kafin bayyanar wannan sanarwar haramta gamgamin a ranar Talatan nan, 'yan sanda ta hanyar amfani da hayaki mai sa hawaye sun tarwatsa matasa masu zanga-zanga da ke kona tayoyi a tituna a kudancin lardin Bacongo da Makelekele kamar yadda wani ganau ya shedar.