1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mahukunta a Kwango sun saki 'yan fafutika

Yusuf Bala Nayaya
December 27, 2016

Darakta a ofishin MDD da ke lura da harkokin kare hakkin bil Adama a kasar ta Kwango Jose-Maria Aranaz, ya ce tabbas an sako 'yan fafutikar sai dai ya na da kokwanto kan makomar sauran.

https://p.dw.com/p/2Uw0w
Demokratische Republik Kongo - Ausschreitungen in Kinshasa
Hoto: Reuters/K. Katombe

'Yan fafutika 19 da aka kamasu lokacin zanga-zangar adawa da gwamnatin Shugaba Joseph Kabila a Jamhuriyar Dimokradiyar Kwango an sakesu a ranar Talatan nan, kamar yadda kungiyoyi da jami'an Majalisar Dinkin Duniya suka bayyana.

Kungiyar Lucha ta tabbatar da cewa mambobinta 18 an sako su bayan da aka kamasu lokacin wani zaman dirshan da suka yi ranar 21 ga watan Disamba a birnin Goma da ke a Gabashin na Kwango, kamar yadda Ghislain Muhiwa wani fitaccen dan fafutika ya bayyana a ranar Talatan nan. Ita ma Gloria Senga, da aka yi garkuwa da ita a ranar 18 ga watan Disamba an saketa a cewar dan fafutikar.