Mahawarar neman sauyi a China na tasiri a yanar gizo | Siyasa | DW | 30.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Mahawarar neman sauyi a China na tasiri a yanar gizo

Masu karfin fada a ji, tsakanin al'ummomin da ke amfani da kafafen sadarwar internet a China sun goyi bayan masu zanga-zangar neman sauyin demokiradiyya a kasar.

Hukumomin kasar China sun jaddada goyon bayansu ga shugabanin yankin Hong Kong a kokarin da suke yi na takawa masu zanga-zangar neman sauyin demokiradiyya birki, wanda suka ce zanga-zangar ba ta bisa kaida. Hakan kuwa na zuwa ne a daidai lokacin da jagoran mulkin na Hong Kong mai cikakken 'yanci ya gargadi jama'ar da suka kawo karshen yamutsin.

Jagoran mulkin na Hong Kong Leung Chun Ying ya gargadi masu zanga-zangar neman sauyin da su kawo karshen yamutsin, wanda ya ce ya hadasa cinkoso na ababen hawa a tsakiyar birnin inda dubban jama'a suka yi cikar kwari

"Ina yin kira ga jama'a da su gaggauta ficewa daga kan titunan da suka datse cikin ruwan sanyi, don kawo karshen cikas din da ake samu akan sha'anin zirga-zirga, ina kira ga wadanda suka shirya wannan zanga-zanga da suka kawo karshenta"

To sai dai duk da irin gargadin da shugabannin suka yi tare da janye 'yan sanda daga fagen daga, masu yin yamutsin sun dage cewar za su ci gaba da mamaye tsakiyar birnin na Hong Kong har sai China ta cika alkawarin da ta yi a shekarun 1997 na kaddamar da sauye-sauye na siyasa, wadanda za su baiwa al'ummar ta Hong Kong damar zabin shugabanninsu da cikakken 'yanci ba tare da yin katsa ladan ba na China a zaben da za a yi kasar a shekarar 2017. Chan Ki Man na daya daga cikin wadanda suka shirya gangami ya kuma ce ba su da niyyar ja da baya

"Wannan abin farin ciki ne dangane da yadda jama'a ke ci gaba da tudada a kan titunan birnin domin yin kokuwar samun demokiradiya ya ce kuna ganin yadda jamaa ke yin kiraye kirayen samar da demokaradiya ya ce muna yin farinciki da abinda ke faruwa a yau"

Tun farko gwamnatin kasar ta china ta hanyar wata babbar jamiarta ta diflomasiya Hua Chunyig ta ce ba za su taba amincewa da tsoma baki na kasahen waje a cikin wannan lamari ba