Mahawara tsakanin Obama da Romney ta zafafa | Siyasa | DW | 23.10.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Mahawara tsakanin Obama da Romney ta zafafa

'Yan takaran shugabancin Amirka, Obama da Romney, sun yi mahawara ta karshe game da manufofin harkokin kasashen ketere.

An yi fafatawa mai yafi, tsakanin shugaban Amirka Barack Obama da abokin karawarsa a zaben da ke tafe Mitt Romnez, yayin mahara karo na uku, kuma na karshe da aka gudanar, kafin zaben kasar ta Amirka.

An gudanar da mahawar ta ƙarshe tsakanin 'yan takaran shugancin Amirka, inda Shugaba Barack Obama na jam'iyyar Demokrat za fuskanci mai adawa da shi Mitt Romney na jam'iyyar Republican, inda aka mayar da hankali kan rawar da ƙasar za ta taka game da manufofin harƙoƙin ƙasashen ƙetere.

Duk da yake mahawarar an shirya bisa manufofin harƙoƙin waje, duk 'yan takaran kan jefa maganar tattalin arziƙi da magance rashin aiki da ya yi wa ƙasar katutu, waɗanda su ne, za su fi jawo musu kuri'un Amirkawa da ke sauraron mahawarar.

USA Rededuell Präsidentenwahl

Muhawara tsakanin Barack Obama da Mitt Romney...

Kuma duk 'yan takaran sun nuna mahimmancin Amirka ga ƙasashen duniya, da yadda za su tunƙari harƙoƙin gabas ta Tsakiya da cinikayya da China, gami da dangantaka da Rasha, da sauran ƙasashen duniya.

Ga yadda Shugaba Barack Obama ya bayyana hanyoyin da aka bi wajen kawar da gwamnatin Marigayi Mu'ammar Gaddafi ta Libiya, bayan mulkin shekaru 42.

"Ina tsammani yana da mahimmanci mu tuna baya, bisa abun da ya faru a Libiya. Na saka a raina ni da dauran Amirkawa, mun shiga gaba wajen hada sauran ƙasashe duniya, kuma ba tare da tura sojoji ba, mun kawar da gwamnati fiye da shekaru 40, da kadaden da ba su fi na wadanda mu ka kashe cikin makonni biyu a Iraki. Kuma wannan ya kashe Amirkawa masu yawa. Kuma bayan abun da za faru a Benghazi, dubban 'zan Libiya sun fito su na nuna goyon baya ga Amirka, na cewa mun tsaya tare da su. Haka ya nuna akwai dama a gaba."

Anasa bangaren dan takarar jam'iyyar Republican Mitt Romney, ya ce tilas Amirka ta sake dabara wajen tunƙaran rikicin da ke faruwa na yankin Gabas ta Tsakiya da sauran ƙasashen Musulmai.

"Mufofi na kai tsaye ne, na neman masu mungun nufi, na tabbatar da katse hanzarin su, kashe su, amma babban abu mai mahimmanci shi ne, aiki da ƙasashen Musulmai domin watsi da zazzafan ra'ayi. Babu bukatar samun wata Iraki, ko kuma Afghanistan. Wannan bai dace da mu ba. Abun da ya dace bin sawun shugabannin masu nuna ƙiyayya ga Amirka, tare da taimakawa sauran ƙasashen Musulmai."

Game da rikicin Syria Shugaba Obama ya yi watsi da zargin kawar da kai.

"Abun da mu ka yi, shi ne neman hadin kan ƙasashen duniya, tare da cewa tilas shugaba Assad ya tafi. Kuma mun zarga wa gwamnatin takunkumi."

Amma Mitt Romney ya ce, abun da Amirka ta yi, ya gaza.

"Na farko, mutane 30,000 gwamnati ta kashe, wannan tabarbarewar aiyukan jinƙai ne. Na biyu kuma rikicin Syria ya bamu damar taka rawa mai mahimmanci cikin zankin Gabas ta Tsakiya."

USA TV-Duell Mitt Romney Barack Obama Boca Raton

.....da masu rufa masu baya

Duk 'yan takaran sun nuna mahimmacin Izira'ila ga manufofin harƙoƙin wajen Amirka, inda shugaba Obama ya bayyana cewa.

"Izira'ila ƙawa ce ta haƙiƙa ga Amirka, babbar ƙawarmu a wannan yankin. Idan aka kai mata hari, Amirka za ta tsaya tare da ita."

Wannan ra'ayi shi ne Romney ya ƙara jaddawa.

"Muddun ina shugaban ƙasar Amirka, za mu tsaya wa Izira'ila. Idan akai wa Izira'ila hari, su na da goyon bayan mu, ba na diplomasiya da al'adu ba kawai, amma harda soja."

Duk yadda ta kasance ranar 6 ga watan gobe na Nowamba, Amirkawa za su tantance shugaba gaba tsakanin mutane biyu shugaba Barack Obama ko kuma Mitt Romney.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Umaru Aliyu

Sauti da bidiyo akan labarin