Mahawara kan yada akida ta sadarwar zamani | Siyasa | DW | 23.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Mahawara kan yada akida ta sadarwar zamani

Taron kafafin yada labarai na duniya na wanda tashar DW ta shirya a rana ta biyu mahalarta taron sun tattauna kan amfani da kungiyoyin 'yan wajan yada akidarsu ta'addan duniya ke yi da hanyoyin sadarwan zamani

Batun irin yanda kungiyar 'yan jihadi ta IS ke yin amfani da hanyoyin sadarwa na zamani irinsu twitter, Google, Face book, Yahoo da sauransu wajan yada akidarta dama rijistan sabbin magoya baya maza da mata, musamman matasa daga kasashen duniya daban-daban, ya kasance a sahun gaban yayin maharar wacce ta samu halartar dimbin jama'a. An dai fara mahawarar ne da haskaka wani majigi na irin sakonnin hotuna ko na bidiyo da kungiyoyin 'yan ta'addar ke yada wa a saman kafofin sadarwar na zamani, da ma hotunan tarin mutane maza da mata daga kasashen Afrika da na Turai dama Amerika ke tururuwa zuwa ga yin mubayi'a ga kungiyoyin 'yan jihadin. Inda suke bada dunguma zuwa fagen daga da sunan yin jihadi. Marie Lamensch wata jami'ar kasar Kanada mai bincike akan lamarin kisan kiyashi dama kare hakin jama'a, daya daga cikin wadanda suka gabatar da laccar bayyana fasahohin da kungiyar IS ke bi wajan yada akidar tata ta irin wadannan hanyoyin sadarwa na zamani.

Ta ce "Da farko dai matasa na amfani da wadannan hanyoyin sadarwa na zamani domin bayyana irin jerin matsalolin rayuwa da suke fuskanta a cikin kasashensu musamman na Turai.To dama kungiyar IS ta mallaki runduna ta musamman ta mutanan da suka kware a cikin wanann aiki da ke bi sau da kafa irin wadannan koke-koke na matasan, nan take sai su fara tuntubar su suna ce masu ku zo muna da maganin matsalolinku. Idan kuna bukatar yin wasu ayyukan agaji ne domin samun tsira ku zo ga inda yara ke mutuwa suna bukatar agajinku. In abokanai ne baku da su, ku zo ga inda ke da akwai soyayya ta Allah da Annabi. Kai dai ko da yaushe suna tunanin samar da amsa ga matsalolin da matasa ke bayyanawa a saman wadannan hanyoyin sadarwa".

To amma da ta ke tsokaci kan wannan matsala Asama Mansur wata 'yar jaridar kasar Tunusiya da ke halatar taro, a cewarta kafofin yada labarai na gargajiya ne ke taimakwa kwarai wajan yada farfagandar da kungiyoyin 'yan ta'addan ke yadawa ta hanyoyin sadarwar na zamani.

"Muna taimakwa kwarai cikin yada manufofin kungiyoyin 'yan ta'adda, domin kullu yaumin za ka tarar ana batun a cikin gidajen radiyo da na talabiji ko a saman mujallu. Wanda ta hakan muke yi masu talla a kyauta. Domin duk abun da ake yawan magana a kansa ya fi jan hankalin jama'a dama haddasa fargaba. Kuma wannan babbar kyauta ce muke yi wa wadannan 'yan ta'adda"

To sai dai yanzu haka kasashe da kungiyoyi da dama ne suka soma tunanin hanyoyin da za'a iya bi wajan dakile mastalar. Inda tuni wasu kasashe suka fara daukar matakan dakile hanyoyin sadarwar na zamani.

Sauti da bidiyo akan labarin