Mahawara kan tazarcen Kagame a Ruwanda | Labarai | DW | 12.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mahawara kan tazarcen Kagame a Ruwanda

Idan har gyaran kundin tsarin mulkin ya yi nasara, a shekara ta 2017 Kagame zai fara wa'adinsa na hudu a gadon mulki, idan ya ci zabe.

A wannan Litini ne majalisar dokokin Ruwanda ke gudanar da wani zama don gyara kundin tsarin mulkin kasar ta yadda shugaba Paul Kagame zai iya yin takara, ya kuma yi tazarce a zaben kasar mai zuwa, wanda ake sa ran yi a shekara ta 2017. Tun bayan kisan kiyashin da aka yi a kasar a shekarar 1994 Kagamen ke mulki a kasar, kuma ya yi nasara a zabukan shekarun 2003 da kuma 2010, a karakashin kundin tsarin mulkin da ke aiki yanzu, wanda kuma ya tanadi da ya kammala wa'adinsa a shekara ta 2017.

Daga farkon wannan shekara dai kusan kashi 60 cikin 100 suka sanya hannu a kan wani korafi, inda suke bukatar shugaba Kagamen ya yi tazarce. Kuma ana hasashen majalisa za ta amince tunda da ma jam'iyyarsa ce ta ke da rinjaye.

Yawancin 'yan kasar dai na mi shi kallon wanda zai tabbatar da daidaito da zaman lafiya bayan kisan kare dangin shkararta 1994 da ma bunkasar tattalin arzikin da ya sauya kasar a shekaru 20 din da suka gabata