1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mahawara kan afuwa ga yan Boko Haram

Usman ShehuApril 5, 2013

Daga ƙarshe dai gwamnatin Najeriya ta kafa wani kwamitin da zai duba batun yi wa ƙungiyar Boko Haram afuwa.

https://p.dw.com/p/18AmT
A photograph made available 23 January 2012 shows Nigerian President Goodluck Jonathan (C) addressing the Emir of Kano (R) during a visit to his palace following the bomb blasts in Kano, northern Nigeria, 22 January 2012. A series of attacks apparently orchestrated by Islamist militants of the 'Boko Haram' group in the northern Nigerian city of Kano on 20 January 2012 have killed more than 160 people according to reports. More than 10 locally made explosive devices were found in abandoned vehicles in the city. A call to stop the violence has been issued by the Kano state government. EPA/STR EPA/STR
Shugaba Goodluck Jonathan da sarkin Kano Ado BayeroHoto: picture-alliance/dpa

Babu dai zato ba kuma tsamanni tsohuwar gwamnatin marigayi shugaba Umar Musa Yaradua ta kai ga gano bakin zaren a cikin rikicin da ya nemi barazana ga daukacin tattalin arzikin kasar. Cikin dan kankanin lokaci ne kuma tasirin sa ya kai har ga iyakokin kasar ta Najeriya da suka fuskanci karuwar kudin shiga a aljihun jihohi da kananan hukumomin kasar, sakamakon shirin afuwar matasan yankin Niger Delta.

Afuwar kuma da ta kai ga sake farfado da ayyukan harkar mai ta kuma kai ga zaman lafiya da kwanciyar hankalin da ta mai da yankin na kan gaba ga batrun cigaban tattalin arziki da rayuwar aluma a daukacin kasar ta Najeriya.

To sai dai kuma da kyar da gumin goshi aka kai ga shawo kan gwamnatin Tarrayar Najeriya da ta amince ta kafa kwamitin nazarin wata sabuwar afuwar ga yan uwansu na boko haram da suka dauki makamai suka kuma tada hankula a daukacin arewacin tarrayar Najeriya. Duk da cewar dai kwamitin na da tsawon wasu kwanaki 14 kafin yanke hukuncin ko afuwar na da fa'ida ga kasar, dama hanyoyin da ya kamaci kai wa ga nassara dai, tuni kasar ta sake rudewa bisa banbancin ra'ayi a tsakanin masu goyon bayan afuwar da kuma ke lale marhabin da matakin mahukuntan na Abuja da kuma kunigyar kiristocin kasar ta CAN da tace an kashe mata yaya da yawa kuma baiwa masu ruwa da tsaki da wannan aiki afuwa baya bisa kaida.

This image taken from video posted by Boko Haram sympathizers shows the leader of the radical Islamist sect Imam Abubakar Shekau made available Wednesday Jan. 10, 2012. The video of Imam Abubakar Shekau cements his leadership in the sect known as Boko Haram. Analysts and diplomats say the sect has fractured over time, with a splinter group responsible for the majority of the assassinations and bombings carried out in its name. (AP Photo) THE ASSOCIATED PRESS CANNOT INDEPENDENTLY VERIFY THE CONTENT, DATE, LOCATION OR AUTHENTICITY OF THIS MATERIAL
Jagoran ƙungiyar Boko Haram, Imam Abubakar ShekauHoto: AP

A baya dai afuwar ta Niger Delta, ta zamo kafa ga dubban yan fafutukar yankin na kaucewa fuskantar tuhumar laifuka dama samun dama na tara abun duniya da kyawun rayuwa, to sai dai kuma a wannan karo har yanzu ana duhu game da me afuwar ta matasan na arewa za ta kumsa, dama irin tasirin da take iya yi ga yakin da ya lamushe rayuka da dama, sannan kuma bashi nuna alamar an gajiya.

A injured man is carried from a United Nation's office after a car blew up in Abuja, Nigeria, Friday, Aug. 26, 2011. A car laden with explosives rammed through two gates and blew up at the United Nations' offices in Nigeria's capital Friday, killing at least seven people and shattering part of the concrete structure. (Foto:AP/dapd)
Harin da Boko Haram suka kai a ofishin MDD dake AbujaHoto: dapd

Har ya zuwa yanzu dai babu bukatun dake kasa a bangaren yayan kungiyar ta Boko Haram da gwamnatin kasar ka iya amfani da su domin nazarin hanyoyin afuwar, sannan kuma ma babu tabbacin an kira sunan ita kanta afuwar da yawun yayan kungiyar da suka dade suna karyata duk wani yunkuri na sulhunta su da gwamnatin kasar. Mallam Garba Umar Kari dai na zaman masanin harkokin zamantakewa a jami'ar babban birnin Tarraya dake Abuja, kuma a cewar sa har yanzu da sauran tafiya a tsakanin kasar da tabbatar da zaman lafiya sakamakon shirin afuwar ta shugaba Jonathan.

Tabbatar da zaman lafiya ko kuma shan shayi abar teburi a tsaka nin gwamnatin da dattawan na Arewa dai, har ya zuwa ranar ta yau dai babu wani martani da ya fito daga yayan kungiyar da tun da farkom ma ba su nuna alamar wata sha'awar yi musu afuwar laifukan da kasar ta Najeriya ke kallon su da aikatawa ba.

Vor den Polizeiposten in Nordnigeria bilden sich oft kilometerlange Autoschlangen. Copyright: Katrin Gänsler Kano, Nigeria, 06.02.2012
Yan sanda ke sintiri a KanoHoto: Katrin Gänsler

To sai dai kuma matakin afuwar daga dukkan alamu na zaman babban sauki ga mahukuntan na Abuja, dake tsaka mai wuyar ci gaba da bada makudan kudi ba tare da gani akasa a cikin yakin da ke kara matsar lokutan zabukan kasar na gaba, ke kuma barazana ga kasar na iya kaiwa ga shirya zabukan a karon farko cikin tarihin yancin kanta na shekaru sama da 50.

Dr Ernest Ereke dai, na zaman wani masanin harkokin siyasa a jami'ar ta Abuja kuma a cewarsa afuwar na iya taimakawa gwamantin kasar ta kowanne fanni. Ereke ya ce:

"Akwai wannan tunanin cewar duk abun da ya shafi hanci to ido ruwa yake yi . Saboda haka duk abun da ya shafi wani bangare na arewa maso gabashin Najeriya to ya shafi daukacin kasar . Saboda haka mun yi asara da yawa, munyi asarar wadanda muke so kuma har munyi asarar dukiya mai yawa a kokarin tabbatar da zaman lafiya a yankin arewa maso gabas , ina da imanin babu wata sadaukar da kan da zata yi yawa a kokarin kawo karshen matsalar. Mun gwada a yankin Niger Delta ba wanda ya yi imanin za ta yi aiki, amma in ka dubi yawan man da ake hakowa a yankin to za ka tabbatar da cewar afuwar ta cima nasarar azo a gani".

Bystanders gather around a burned car outside the Victory Baptist Church in Maiduguri, Nigeria, Saturday, Dec. 25, 2010. Authorities say dozens of assailants attacked the church on Christmas Eve, killing the pastor, two members of the choir and two people passing by the church. Police are blaming members of Boko Haram, a radical Muslim sect. (AP Photo - Njadvara Musa)
Wata mota da Boko Haram suka tarwatsa da bom a MaiduguriHoto: AP

Sama da Naira miliyan dubu 400 ne dai gwamnatin ta ware domin kasafin tsaron kasar da kusan kaso 80 cikin dare ya kare a cikin yankin da rabin wadannan kudade ke iya sauya rayukan daukacin alumarsa.

Mawallafi: Ubale Musa

Edita: Usman Shehu Usman