Maharin New Zealand ya musanta zargi
June 14, 2019Talla
Matashin da ya bude wuta kan masallata a tagwayen masallatai a birnin Christchurch na kasar New Zealand a watan Maris ya ki amincewa da laifukan kisan kai da aikata ta'addanci da ake zarginsa da aikatawa.
Alkalin da ke sauraron shari'ar ya ce babu rashin lafiyar kwalkwalwar da ke damun maharin da zai iya hanashi fuskantar shari'a. Akalla mutane akalla 50 ne suka mutu tare da jikkata wasu da dama a harin da dan bindigan ya kai, kuma shi ne hari mafi muni a tarihin kasar New Zealand a baya-bayannan, matakin da ya sa kasar sake kwaskware dokokin mallakar bindiga.