1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Al'umma a Jihar Zamfara na cikin fargaba

Zulaiha Abubakar
September 13, 2018

Rahotanni daga jihar Zamfara sun bayyana rasuwar mutane 13 yayin da wasu ke kwance asibiti cikin mawuyacin hali sakamakon wani mummunan hari da 'yan bindiga suka kai kauyen Badarawa da ke karamar hukumar Shinkafi.

https://p.dw.com/p/34oLc
Flüchtlinge im nigerianischen Bundesstaat Zamfara
Hoto: DW/Y. Ibrahim

Rundunar yan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da afkuwar lamarin a ta bakin kakakin ta SP Shehu Muhammad. Wakilin DW a Zamfara Yusuf Ibrahim Jargaba, ya bayyana cewa kakakin 'yan sandan ya kara da cewar jami'an tsaro ba su yi kasa a gwiwa ba, suna samun labarin harin suka garzaya yankin da lamarin ya faru, ya kuma jaddada alwashin rundunar na ganin an gano wadanda suka aikata wannan hari, don su girbi abinda suka shuka.