Kanta wakili ne na Sashin Hausa na DW da ke aiko da rahotanni daga birnin Yamai a Jamhuriyar Nijar.
Mahamn Kanta shi ne wakilin Sashin Hausa na DW da ya fi kowanne dadewa yana aiko da rahotannin kan abubuwan da ke faruwa a nahiyar Afirka. A zamanin da ya yi yana wannan aiki ya ga sauye-sauye da dama da suka danganci aiko da labarai.